ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa an kaddamar da cibiyar ne tare da halattar manya-manya jami’an ma’aikatar sadarwa ta kasa wadanda suka hada da ministan sadarwa da fasahar zamani, Mohammad Javad Azari Jahromi, da kuma wasu ‘yan majalisar dokokin kasar.
A jawabinda ya gabatar a bikin kaddamar da cibiyar, wacce aka sanyawa suna “Cibiyar tattara bayanan yanar gizo ta Shahid Qasim Sulaimani” Jahromi ya ce, cibiyar ta na da karfin ajiya da musayar bayanai na na’urori masu kwakwalwa mai saurin terabite guda a ko wani secon.
Ministan ya kara da cewa cibiyar za ta taimaka wajen magance matsalolin rashin karfin yanar gizo ko Internet a cikin gida, da kuma kare bayanai daga kutsen makiya daga ciki ko waje.
Ministan ya kara da cewa an gina cibiyar a cikin watanni 6 kacal, kuma yana da server-server har guda 500 guda biyu, wadanda zasu taimakwa wajen sauwaka bincike ta internet a cikin gida.
342/